Kotu ta yankema Amira watanni goma shabiyu na gwajin hali

0
464

A ranar Laraba ne, 29 ga watan Yuni, Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2 da ke Abuja ta sallami Ameerah Sufiyan, wadda ta yada labarin karya na cewa an yi garkuwa da ita ta.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Amiran mai shekaru 23 a Apo Resettlement Abuja da laifin bayar da bayanan karya, da nufin bata ma’aikatan gwamnati. Ta amsa laifin da ake tuhumar ta.

Alkalin kotun, Chukwuemeka Nweke, a hukuncin da ya yanke, ya ce ya sallame ta ne bisa tanadin sashe na 454 na dokar shari’a ta ACJA, 2015.

“Bisa rahoton gwajin da aka yi mata na cewa ba ta cikin tunani mai kyau a lokacin da ta aikata laifin, an sallame ta da wasu sharudda.

Na farko, “dole ne wadda ake tuhuma ta kasance a kan gwaji na tsawon watanni 12 na kalanda.

“Na biyu kuma, za a saki wadda ake kara zuwa ga waliyyinta, sannan kuma za a sanyata a karkashin kulawar jami’in binciken kwakwaf, DCP Hauwa Ibrahim, domin ta sa ido a kan ta.

“Na uku, dole ne ita jami’in tsaron ta dinga kai rahoto kowane wata zuwa hedkwatar ‘yan sanda, Abuja, don tantance halinda ake ciki.”

Cewar kotun.

Leave a Reply