Buni ya nada Yusuf Ali mataimaki na musamman

1
491

Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya amince da nadin Yusuf Ali, a matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) akan hanyoyin sadarwa na zamani da dabarun sadarwa.

Yusuf Ali, kwararre ne a harkar buga labarai na gargajiya da na zamani. Kafin zuwan wannan nadin, jami’in yada labarai ne na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hedikwatar Abuja.

Read also

Read also: Yadda Ahmed Musa captain din super eagle ya raba tallafi https://neptuneprimehausa.com/?p=23519

Ya yi aiki nagari da Gwamna Buni – ya jagoranci jam’iyyar APC CECPC wanda ya sake gina jam’iyyar tare da sauya sheka da Sanata Abdullahi Adamu – wanda ya jagoranci kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar APC.

A matsayinsa na babban mataimaki na musamman ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni, kan harkokin sadarwa na zamani da dabarun sadarwa, Yusuf zai kawo shekarunsa na gogewa a harkar sadarwa na zamani don bunkasa, da aiwatar da dabarun sadarwa mai lasisi, wanda ya hada da yada dimbin ayyuka da kokarin mai girma Gwamna, ta hanyar Yanar Gizo, sannan shi ze zama tushen samun bayanai, gami da gidajen yanar gizon ƙungiyoyin labarai a duka shafukan yanar gizo, da kafofin watsa labarun intanet.

Ana sa ran zai yi nasara a ayyukan da ke gabansa, wanda ake kyautata zaton zai aiwatar da su ta hanyar bayyana komi a fili, ta hanyar rikon amana da kwarewa, yadda ze gamsar da mai girma Gwamna, Mai Mala Buni, wanda a kullum yake aiki tukuru don kyautata rayuwar mutanen jihar Yobe.

Nadin ze fara aiki nan take.

1 COMMENT

Leave a Reply