Kisan Nafi’u: An sake gaurfanar da Hafsat Chuchu a gaban wata kotun

0
84

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 3 ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan ta sake gurfanar da matar nan Hafsat Sani Suraj da ake zargi da kisan wani hadimin gidanta mai suna Nafi’u Hafiz.

An sake gurfanar da wacce ake zargin ne bayan da aka ɗauke shari’ar daga gaban kotun Mai Shari’a Zuwaira Yusuf.

Lauyan gwamnati wanda ke gabatar da ƙara, Barista Halima Yahuza Ahmad ta shaida wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Disamba, 2023 Hafsa Suraj ta yi amfani da wuka inda ta caccaka wa marigayin a kirjinsa da wasu sassa na jikinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Ana tuhumar Hafsat Suraj da laifin kisa, laifin da ya saɓa da sashe na 221 na kundin pinal kod.

Sai dai Hafsat wadda aka fi sani da Hafsat ChuChu ta sake yin gum da bakinta yayin da aka tambaye ta ko ta fahimci abin da takardar ƙarar ta ƙunsa.

Lauyan da ke kare ta, Barista Sani Ammani ya nemi kotun da ta bayar da umarnin gwada kwakwalwarta a Asibitin Masu Larurar Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya don sanin shin ko tana da lafiyar da za a iya yi mata shari’a dogaro da sashe na 278(3) na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na shekarar 2019.

Sai dai masu gabatar da ƙara sun soki roƙon na lauyan masu kariya, inda suka nemi kotun ta ɗauki wacce ake ƙara a matsayin ta musanta zargin aikata laifin.

A yayin haka kuma, kotun ta gurfanar da ƙarin mutane uku da suka haɗa da mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da kuma Adamu Muhammad da Nasidi Ibrahim da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifi tare da ɓoye gaskiyar lamarin da bayar da bayanan ƙarya game da dalilin rasuwar marigayi Nafi’u.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta sa a duba ƙwaƙwalwar Hafsat Chuchu

“Waɗanda ake zargin sun yi amfani da bayanan ƙarya wajen sanar da ’yan uwan Nafi’u game da dalilin rasuwarsa inda suka ce ya rasu ne dalilin aikin basir da aka yi masa.”

Waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da shi da suka saba da sashe na 97 da 277 da 178 na kundin pinal kod.

Har ila yau, masu gabatar da ƙarar sun nemi kotun da ta cire sunan wanda ake ƙara na huɗu, wato Malam Nasidi Muhammad daga cikin jerin waɗanda ke fuskantar shari’ar.

Sai dai lauyoyin kariya, Barista Sani Ammani da Barista Haruna Magashi da Barista Fauziyya Yusuf sun yi suka kan wannan roƙon.

Lauyoyin sun ce Kwamishinan Shari’a ne kaɗai yake da wannan damar na cire sunan wani daga cikin shari’a dogaro da sashe na 124 da 125 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka.

Bayan sauraron ɓangarorin ne Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Faruk Lawan ya bayar da umarnin tsare waɗanda ake zargi a gidan gyaran hali.

Kazalika, ya ɗage sauraren shari’ar zuwa wata rana da ba a ambata ba don yanke hukunci kan batun cire sunan wanda ake zargin daga cikin shari’ar.

Leave a Reply