Muhimmancin ranar ‘Good Friday’ ga addinin kirista

0
78

A yayin da Kiristoci a faɗin duniya baki ɗaya ke fara shirin gudanar da bukukuwan Istan wannan shekar, fastoci na bayyana muhimmancin Good Friday kamar yadda Bishara mai tsarki ta nuna.
A zantawarsa da manema labarai, inda ya yi ƙarin bayani kan muhimmancin wannan rana, Fasto Abdoulkader Korao na Church Eglise Assemblee de Dieu ta n’guwar Nouveau Marche dake birnin Yamai, y ace “Yesu Almasihu ya zo ya mutu an giciye shi duk da bai yi wani laifi ba. Saboda mu ya mutu, kuma mutuwarsa ya ɗauki dukkan zunubanmu saboda mu samu fansa da ‘yanci. Ma’anar wanna rana Kenan, saboda mu samu bangaskiya a gareshi, mu kuma samu shiga mulkin Allah.

“An giciye Shi a ranar Juma’a amma a ranar Lahadi Ya tashi daga matattu”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk da addu’o’i da ake yi a faɗin majami’o’i, “kowane iyali na shirin da za su yi na wannan hidima ta Ista. Abin da zamu tunace kowani Kirista shi ne a kaucewa duk abin da zai samu cikin zunubi. Ku kuma shirya zukatanmu a gaban Ubangiji, mu samu sulhu da shi.

“Mu samu zaman lafiya, mu kuma kasance masu ba da zaman lafiya”, a cewarsa.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya taya kiristoci murnar bikin Ista

Ranar Good Friday ko kuma Vendredi Saint a Faransance na daga cikin mahimman ranakun shekara a wajen mabiya addinin Kirista abin da ya sa ake ƙiranta juma’a mai mahimmanci.

Ranar kan zama wata damar yawaita ibada domin neman albarkar ubangiji har ila yau.

Wani abin da ke ƙara fayyace mahimmancin wannan lokaci Kiristoci na ɗarikar katolika a nasu ɓangaren kan kammala azumin da suke gudanarwa a tsawon kwanaki 40 na kowace shekara.

Adamou Maidaji wani matsahin Kirista ne a majami’ar Eglise Evangelique na ɗaukan wannan Juma’a ta good Friday da mahimmancin gaske.

A bana bukukuwan sallar Easter ko Pacques na zuwa a wani lokacin da Nijer da al’ummarta suka fuskanci ƙalubale da dama sakamakon hatsaniyar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Adamou Maidaji na Alfahari da tasirin addu’oi kan yanayi da aka shiga a ƙasar saboda haka za su ƙara azama akan irin wannan aiki.

Kamar yadda aka saba kristoci za su hallara a majami’u domin raya dare a wannan Juma’a kafin su ci gaba da addu’oi a ranar Lahdin dake tafe yayinda ranar litinin 1 ga watan Afrilu wato ranar sallar Pacques ko kuma Easter ke zama ranar hutu a wajen ma’aikata a hukumance.

Leave a Reply