Hisbah ta kori jami’inta kan haɗa kai da masu baɗala a Kano

0
163

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kori ɗaya daga cikin hafsoshintta da ta samu da laifin yi mata zagon ƙasa a aikin da take yi na kawar da baɗala a jihar.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa hukumar na neman korarren hafsan Hisbar ruwa a jallo, kan laifin haɗa kai da ɓata-gari wajen taimaka wa masu ayyukan ɓarna a jihar.

Sheikh Aminu Daurawa ya ƙara da cewa Hukumar na binciken wasu ma’aikatan nata su biyar da ake zargi da sa hannunsu a cikin wannan badakala.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Kano ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da auren jinsi

Daurawa ya bayyana cewa “mun kori Mataimakin Sufurtanda na Hisbah (DSH) inda kuma muke neman sa ruwa a jallo. A duk lokacin da muka same shi, to za mu kama shi tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

“Abin da yake yi shi ne yana haɗa baki da masu otel-otel don kada a kai wa otel ɗinsu sumame.

“To lokacin da muka kai suname irin waɗannan otel sai suka ji haushi cewa bayan sun biya shi kuɗi, ga kuma abin da ya faru.

“Akwai wani ma a cikinsu da ya ce mana mu gaya masa duk abin da muke so zai taimaka mana; Mun gaya masa cewa gwamnati ce ta ɗora mana nauyin gudanar da wannan aiki da muke yi.”

Shaikh Daurawa ya ƙara da cewa “ba mu zuwa kowane sumame sai mun bi wasu matakai, bayan mutanen unguwa sun aiko mana da takardar sanarwa game da abin da ke faruwa a kusa da su tare da sa hannun akalla mutane biyar daga unguwar.

“Sai mun tura masu yi mana binciken sirri don mu gano gaskiyar abin da aka sanar da mu. Sannan sai mu sanar da DPO na yankin sannan sai mu sami takarar iznin shiga wurin.“

Leave a Reply