Connect with us

Labarai

An sako matan shugaban ƙaramar hukumar da aka sace a Jigawa

Published

on

Wadanda suka sace matan Shugaban Ƙaramar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa, Nasiru Ahmad, su biyu, sun sake su.

An sace matan ne a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi a ƙarshen makon da ya gabata.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ne ya tabbatar da sako matan biyu da maraicen Talata.

Ya ce bayan sakin nasu, an garzaya da su babban asibitin Dutse domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace matan shugaban ƙaramar hukuma

Sai dai bai yi ƙarin haske a kan ko an biya kuɗin fansa ba kafin a saki matan.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne wasu ’yan bindiga suka kutsa kai gidan Ciyaman ɗin, sannan suka yi awon gaba da matan.

Maharan sun shiga garin ne da dare inda suka dinga harbi babu kakkautawa, kafin daga bisani suka shiga gidan kai-tsaye suka tafi da matan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Ningi

Published

on

Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Ningi

Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Ningi

Majalisar Dattawan Najeriya ta yafe wa Sanata Abdul Ahmed Ningi tare da janye dakatarwar da ta yi masa tun daga ranar 12 ga watan Maris.

Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan Sanata Abba Moro ya gabatar da ƙudirin neman afuwarta a madadinsa kuma “ya ɗauki alhakin dukkan” abin da ya faru a zaman da suka yi yau Talata.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya siffanta Ningi a matsayin “mai hazaƙa” kuma ya ce sun ɗauki matakin ne “ba tare da nuna ɓangaranci ba”.

KU KUMA KARANTA: Majalisa ta dakatar da sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku

Dakatarwar da aka yi wa sanatan mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya ta tsawon wata ta jawo cecekuce a majalisar da ma faɗin ƙasar a watan Maris.

Ƙudirin da majalisar ta zartar a lokacin ya zargi Abdul Ningi da “zubar da ƙimar majalisa” bayan ya zargi shugabanninta da sake yin wani kasafin kuɗi na 2024 bayan wanda ‘yan majalisar suka amince da shi a bainar jama’a.

Continue Reading

Ilimi

Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

Published

on

Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa - Dauda Lawal 

Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal

Daga Idris UMAR, Zariya

Gwamna Dauda Lawal ya halarci taron yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu na Jami’ar tarayya, wanda ya gudana a filin taro na Jami’ar da ke Gusau a cikin satin da ya gabata

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya shelanta bayar da gurbin karatu ga duk wanda ya zo na ɗaya a Jami’ar.

Cikin jawabinsa a wurin taron, Gwamnan ya yaba wa shugabannin Jami’ar game da yadda suka iya ririta ɗan abin da suke da shi, duk da ɗimbin ƙalubalen da suke fuskanta.

Ya ce, “Ina matuƙar farin cikin kasancewa da ku yau a wannan bikin yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu a wannan jajirtacciyar Jami’a, Jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau.

Ina taya jami’ar nan murnar samun wannan nasara, duk kuwa da matsalolin da suke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta. Ina kuma yaba wa iyaye da ɗalibai bisa sadaukarwar da suka nuna har zuwa wannan matsayi.

Muna sa ran samun makoma mai kyau kuma mai albarka duk da tarin ƙalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jiha kuma al’umma.

Muna yin addu’a kuma muna aiki ba dare ba rana don samar da makoma mai kyau. Duk waɗannan matsaloli za su wuce da izinin Allah Maɗaukakin Sarki.”

Gwamnan ya yi ƙarin haske kan ƙoƙarin gwamnatinsa na gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara bayan kafa dokar ta-ɓaci a bara.

“A matsayinmu na gwamnati, mun ƙuduri aniyar ilimantar da duk ’ya’yan Zamfara. Ilimi shi ne ginshiƙin da ke haskaka ruyuwar ɗan adam.

“Mun ware maƙudan kuɗaɗe ga ɓangaren ilimi a cikin kasafin kuɗinmu na 2024 kuma muna fatan za mu kai ga babban matsayi a 2025, 2026, da 2027. Muna fatan cimma kashi 25 zuwa 30 na haɓaka tsarin ilimi.

Tare da samar da ingantaccen tsari a fannin da sarrafa albarkatun da ya ƙunsa, muna da ƙwarin gwiwar cewa za mu farfaɗo da ababen more rayuwa, ɗaukar ƙwararrun malamai, horarwa da sake horar da waɗanda ake da su.

“Za kuma mu ƙara yawan masu karatu a makarantun firamare da na gaba da firamare ta hanyar wayar da kan jama’a da samar da ingantattun wuraren koyo da koyarwa. Ilimi kyauta ne, kuma muna fatan ya zama wajibi ga kowa.

“Mun kuma yi wa manyan makarantunmu da ke jihar kason kuɗi mai yawa don fara aikin gyara su zuwa matakai masu inganci.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

A karon farko Jami’ar Jihar Zamfara na shirye-shiryen amincewa da shirin Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa.

Mun umurci ’yan kwangilar da gwamnatin da ta shuɗe ta tilastawa barin wuraren aiki da su koma bakin aiki, kuma muna fatan nan da watanni masu zuwa, rukunin dindindin na jami’ar zai fara aiki. A lokaci guda, NUC za ta amince ga duk kwasa-kwasai.

“Mun karɓi mulki a jihar da gwamnati ta ƙi biyan kuɗaɗen jarrabawar WEAC da NECO har na biliyoyin Naira fiye da shekaru uku.

Dole muka yi shiri na musamman da hukumomin, kuma tun daga lokacin an fara biyan kuɗi a kan kari kuma za a kammala su a kan lokaci.

“A cikin ƙarancin albarkatunmu, za mu ci gaba da bayar da taimako ga jami’a. Burinmu shi ne mu ƙara haɓaka ilimi a jiharmu ta yadda za a samu damarmaki ga ɗaukacin matasanmu da za a horar da su don kai ga ƙololuwar da ilimi ke samarwa.”

Continue Reading

Labarai

Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

Published

on

Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin sufurin jirgin samanta na Air Nigeria, har sai Baba ta gani.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, ne ya sanar da hakan yayin taron Ministoci na cika shekarar Tinubu, guda a kan mulkin ƙasar.

Ya ce, matakin ya zo ne, lura da cewa kamfanin a ko da yaushe yunkurin yin amfani da jiragen saman wasu ƙasashen waje ya ke a matsayin na ta.

Idan za a iya tunawa, a shekarar 2023 ne, ma’aikatar sufurin jiragen sama, ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan sufuri, Hadi Sirika, ta ƙaddamar da kamfanin jirgin mallakin Najeriya, wato Nigerian Air kwanaki uku kafin ƙarshen wa’adin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Lamarin dai ya yanwo cece-kuce a tsakanin al’ummar ƙasar, la’akhari da yadda daga bisani aka gane cewa akwai kuskunda a cikin batun.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like