Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100

0
97

A yayin taronsu na farko a wannan shekara, kwamitin Harkokin Kuɗi na Babban Bankin Najeriya ƙarƙashin gwamnan bankin CBN, ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100.

A wata sanarwar da CBN ta wallafa a shafinta na kafar X, an sanar da cewa gwamnan bankin Olayemi Cardoso, ya ƙuduri aniyar tsuke bakin hada-hadar kuɗaɗen ruwa, inda ya yi ƙarin awon MPR zuwa kashi 22.75% daga kashi 18.75% cikin 100.

Gwamnan bankin ya sanar da hakan ne ranar Talata bayan taron kwamitin da ya gudana a birnin tarayyar Najeriya, Abuja, inda hedikwatar babban bankin take. An bayyana cewa duka mambobin kwamitin su 12 sun amince da wannan mataki.

A nazarin tattalin arziki, ƙara kuɗin ruwa wani mataki ne da ke da manufar janyo hankalin masu ajiyar kudi a bankuna, don su ƙara yawan kuɗaɗen da suke ajiyewa a asusun ajiya da bankuna ke biyan kuɗin ruwa kan ajiya.

Idan yawan masu ajiye kuɗi a asusun banki ya yawaita, to za a samu raguwar adadin kudi da ke yawo a hannun mutane, wanda yawan shi ne ke zaman daya daga musabbaban da ke kawo raguwar darajar kuɗin ƙasa, da hauhawar farashi.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umurci CBN ta biya wani Bajamushe naira Miliyan 63 da ta tsare ba bisa ƙa’ida ba

A wani ɓangaren kuma, ƙara kuɗin ruwa yakan rage yawan masu cin bashin banki, wadanda za su ga tsadar cin bashin, musamman idan sun kwatanta da ribar da za su iya samu ta amfanin da kudin bashin don kasuwanci, ko yin wata hada-hadar kuɗi.

Kafin wannan sabon mataki na CBN, yawan kuɗin ruwa da aka ƙayyade a kasar shi ne kashi 18.75, tun bayan taron kwamitin da ya gudana a watan Yuli na shekarar 2023.

Da ma dai alhakin babban bankin ƙasa ne ƙayyade kuɗin ruwa da bankunan da ke ƙasa za su caji masu karɓar bashi, walau kamfanoni, ko gwamnatoci, ko ɗaiɗaikun mutane da ke hada-hadar kuɗi a ƙasar.

Babbar manufar ƙayyade kudin ruwa ita ce sarrafa yawan kudade da ke hannun mutane. Ana ƙoƙarin rage yawan kuɗin da ke yawo a tattalin ariziki don shawo kan hauhawar farashi, ko kuma a ƙara yawansa don haɓaka cinikayya da hada-hadar kuɗi a tattalin arziki.

A zaman kwamitin da Mista Cardoso ya jagoranta, an kuma kara mafi ƙarancin adadin tsabar kuɗin da ake buƙatar bankunan kasuwanci su ajiye a lalitarsu zuwa kashi 45 cikin 100, na kason jimillar adadin kuɗaɗen ajiya da kwastomomin bankin suka zuba a asusun kowane banki.

Haka kuma, an bar adadin ƙarfin iya biyan bashi da bankuna ke da shi a kashi 30 cikin 100, wanda adadi ne da ake aunawa da yawan tsabar kudi da bankuna ke da shi idan an kwatanta da bashin da ake bin su.

Leave a Reply