Labarin yana gefen ku!

Biden da Trump sun yi nasara a Michigan a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyunsu

3

Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban ƙasar Donald Trump sun samu nasara a zaɓen fitar da gwani na Jihar Michigan, lamarin da ya ƙara ƙarfafa yiwuwar cewa ƴan siyasar biyu ka iya sake haɗuwa a zaɓen shugaban ƙasa.

Biden ya kayar da ɗan majalisar Minnesota Dean Phillips, wanda shi ne babban mai hamayya da shi da ya yi saura a Jam’iyyar Democrat.

Ƴan Democrats ɗin sun riƙa sa ido dangane da zaɓen na Michigan ganin cewa jihar ce matattara ta mambobin jam’iyyar masu goyon bayan Biden waɗanda suka kai shi ga nasara a zaɓen 2020 kuma suke ganin a yanzu kamar sun tura mota amma ta bule su da ƙura.

Ga Donald Trump, a halin yanzu ya lashe jihohi biyar a jerin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta Republican take yi.

Nasarar da ya samu a Michigan kan babbar abokiyar hamayyarsa wadda tsohuwar jakada ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Nikki Haley, na zuwa ne bayan tsohon shugaban ƙasar ya kayar da ita a mahaifarta ta South Carolina ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: Rikici ya kaure tsakanin Biden da Netanyahu kan hare-haren Gaza

Yaƙin neman zaɓe na Trump na neman goyon bayan wakilai masu zaɓe1,215 da ake buƙata domin ganin ya samu tikitin takarar shugabancin ƙasar.

A shekarar 2020 ne aka gudanar da zaɓen Shugaban Amurka na ƙarshe inda Joe Biden na Jam’iyyar Democrats ya kayar da shugaba mai ci na wancan lokacin Donald Trump na Jam’iyyar Republican.

Bayan saukarsa daga mulki, Donald Trump ya sha fuskantar shari’o’i daga ciki har da zarginsa da ajiye wasu takardun sirri na ƙasa da zarginsa da yin katsalandan a zaɓen ƙasar na 2020.

Sai dai Mista Trump ya musanta waɗannan zarge-zargen inda ya ce duk bi-ta-da-ƙullin siyasa ce.

Leave A Reply

Your email address will not be published.