APC ta bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga waɗanda bala’in gobara ya rutsa da su a kasuwar Maiduguri

1
270

A ranar Juma’a ne jam’iyyar APC ta bayar da gudummawar naira miliyan 100 ga waɗanda bala’in gobarar kasuwar litinin ta Maiduguri ya rutsa da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Sen. Abdullahi Adamu ne ya bayar da tallafin a lokacin da kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya kai ziyarar jaje ga gwamnan Borno, Babagana Zulum.

Adamu ya ce jam’iyyar APC ta bayar da gudunmawar naira miliyan 100 domin tallafa wa gwamnati wajen bayar da agaji ga waɗanda gobarar ta shafa da ta afku a ranar lahadi.

Shugaban jam’iyyar ya samu rakiyar Sen. Abubakar Kyari, mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa shiyar Arewa; Amb. Usman Sarki, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa; Amb. Habib Habu, mai ba da shawara na musamman kan yarjejeniya da shirye-shirye; da Nata’ala Keffi, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya jajantawa gwamnati da jama’ar Borno kan gobarar kasuwa

A nasa jawabin, Zulum ya mika godiyarsa ga shugaban jam’iyyar APC da tawagarsa bisa ziyarar da suka kai Borno domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa. Gwamnan ya ce ƙuɗaɗen da jam’iyyar ta bayar zai taimaka matuka wajen rage raɗaɗin waɗanda abin ya shafa.

Hakazalika, sakamakon gobarar da ta ƙona shaguna da dama a babbar kasuwar litinin ta Maiduguri a safiyar
lahadin da ta gabata, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar jin ƙai da ci gaban jama’a ta kai ziyarar jaje ga gwamnatin jihar tare da bayar da tallafin kayan abinci ga wadanda abin ya shafa.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda abin ya shafa tare da bayyana cewa za a fara aikin sake gina kasuwar a cikin makon nan.

1 COMMENT

Leave a Reply