An Cafke Mutumin Da Ya Kashe ‘Ya’yansa 3

0
314

Daga Rabo Haladu

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Enugu ta kama wani mutumi mai suna Ifeanyi Amadikwa bisa zarginsa da kashe ƴaƴansa mata uku.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar, mutumin mai shekara 52 bayan ya kashe ƴaƴan nasa, sai ya saka su a cikin wata lalataccen firinji.

Binciken da ƴan sandan suka yi sun gano cewa mahaifiyar yaran ta je kasuwa da ɗansu namiji ɗaya kacal, amma bayan ta dawo sai ta nemi ƴaƴanta mata ta rasa.

Sai dai a yayin da take nemansu, sai mijin matar wanda shi ake zargi, sai ya yi ta abubuwan da suka ja hankalin matar wajen firinjin wanda ya dawo da shi daga shagonsa.

Bayan da matar ta duba da kyau, sai ta ga gawarwakinsu a cikin firinjin inda ta ga akwai alamun duka a jikinsu.

A halin yanzu ƴan sandan dai na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar wannan lamari

Leave a Reply