Hatsaniya Ta Barke A Shalkwatar APC, Masu Zanga-Zanga Na Sukar Shugaban Jam’iyyar

0
535

Daga; Rabo Haladu.

WANI rikici ya barke a shalkwatar Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da ke Abuja a ranar Alhamis.

Wasu matasa masu zanga-zanga sun hallara a ofishin jam’iyyar inda rahoton  ke nuna cewa masu zanga-zangar sun rika yin wakoki suna sukar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

rahoton ya ce matasan sun fito daga Jihar Kogi ne, kuma sun isa shalkwatar ne yayin da jam’iyyar ke wani taro.

Masu zanga-zangar na nuna bacin ransu ne kan abin da suka kira “kwace tikitin takarar mukamin dan majalisar wakilai da aka yi wa wani gwaninsu” kuma aka mika shi ga wani mutumin na daban.

Jami’an tsaro sun kulle kofofin babban ofishin jam’iyyar yayin da suka ji masu zanga-zangar na ikirarin hana Abdullahi Adamu ficewa daga ginin.

Leave a Reply