Ya Yi Wa ‘Yar Makwabcinsa Yanka Rago

0
457

Daga Rabo Haladu

Rundunar ‘yan sandan reshen Jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mazaunin Ƙaramar Hukumar Tofa da ke jihar bisa zargin yin garkuwa da wata yarinya mai suna Zuwaira Gambo kuma ya yanka ta a garin Sabon Fegi a dai garin Tofa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu gawar yarinyar mai shekara 13 ne a wani kango da ke garin Tofa, kwana guda da ɓatan ta.

Haka zalika ta ce ta kama matashin ne bayan sama da kwanaki dari biyu da faruwar al’amarin, a lokacin da yake shirin karbar kudin fansar kanin marigayiyar.

Matashin dai mai suna Auwwalu Abdulrashid, mai shekara 2, wanda ake wa laƙabi da Lauje, yana makwabtaka da gidansu wadda ake zarginsa da kashewa, kamar yadda mai magana da yawun rundundar ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana.

Tun bayan da ya yi garkuwa da yarinyar, ya buƙaci a ba shi naira miliyan guda a matsayin kuɗin fansa, amma bayan an yi ciniki an tsaya kan dubu 400. Amma ana tsaka da cinikin kawai sai aka ga gawarta an yar da ita a wani kango.

Shi ma mahaifin yarinyar cikin kuka ya yayi bayanai  yadda ya samu gawar yarinyarsa inda ya ce yana dab da zuwa biyan kuɗin fansar ƴarsa ya samu labarin an kashe ta inda ya tarar da ita an yanke mata maƙogwaro sa’annan an rufe mata baki.

A cewar Kiyawa, bayan binciken da suka yi, wanda suka kama ya tabbatar musu da cewa shi ya kashe Zuwaira, a cewarsa “ya yaudare ta, ya kai ta kango, sannan kuma ya ɗauki hijabinta ya shaƙe mata wuya ya ɗauko wuƙars ya yankata.

A cewar Kiyawa,sai bayankwanaki sama da 200 da faruwar wannan lamarin asirin wanda ake zargin ya tonu bayan wanda ake zargin ya yi garkuwa da ƙanin marigayiyar mai suna Muttaƙa inda ya nemi a ba shi naira miliyan biyu.

baya sai aka ba shi naira dubu 100 ya saki yaron, inda aka ɗauko yaron a wata makarantar firamare da ke Dawanau.

Leave a Reply