Almajirai 9 sun rasa ransu a Birnin Kebbi

0
90

Daga Idris Umar, Zariya

Al’ummar unguwar Badariyya da ke cikin garin birnin Kebbi a safiyar ranar Asabar ɗin nan, sun wayi gari cikin firgici sakamakon mutuwar wasu almajirin har su 9 rigis lokaci guda.

Wani mazaunin unguwar ya bayyana wa manema labarai cewar, almajiran sun gamu da ajalinsu ne baki ɗaya a dalilin Ibtila’in ruguzowar wani ɓangaren Dutsi da ake ƙira Dutsen-Dukku, wanda ya raba tsakanin birnin Kebbi da garin Tarasa a kan almajiran su 9.

KU KUMA KARANTA: Mutum 3 sun rasu, an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe

Almajiran waɗanda suke a makarantar wani Malamin Allo mai suna Malam ɗan Ummah, tuni an tonosu da shirin yi masu jana’iza.

Jama’a suna ta nuna alhininsu akan lamarin.

Leave a Reply