Labarin yana gefen ku!

Ko yaya za ta kaya tsakanin EFCC da Yahaya Bello?

1

Al’ummar jihar Kogi a Najeriya da masana kundin tsarin mulkin ƙasar na ci gaba da yin tsokaci akan dambawar dake tsakanin tsohon Gwamnan jihar Alhaji Yahaya Bello da hukumar EFCC.
Hukumar ta EFCC dai ta cafke Yahaya Bello ne a gidansa dake Abuja bisa zargin yayi sama da faɗi da Naira biliyan 84 lokacin da yake Gwamnan jihar Kogi.

Rahotanni dai sun nuna cewa Yahaya Bello ya kuɓucewa hukumar ta EFCC ne bisa gudumuwar da ya samu daga Gwamnan na Kogi mai ci Usman Adodo.

KU KUMA KARANTA:EFCC na tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi kan almundahana

A hirar shi da manema labarai, shugaban jam’iyyar APC a Lokoja Alhaji Maikuɗi Bature ya ce babu wani laifi da Yahaya Bello yayima ‘yan jihar Kogin sai dai masu yi mashi bita da ƙulli irin ta siyasa.

Masana kundin tsarin mulkin ƙasar na ganin lamarin dake tsakanin EFCC da Yahaya Bello akwai buƙatar yin taka-tsantsan.

Da ya ke tsokaci game da lamarin, Barista Mainasara Kogo Umar lauya mai zaman kansa a Najeriya ya ce hatta matakin da Gwamnan Usman Adodo ya ɗauka karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

A yanzu dai al’ummar jihar Kogin dama sauran ‘yan Najeriya na ci gaba da zuba idanu domun ganin yadda za a kwashe tsakanin tsohon Gwamnan Kogin Yahaya Bello da kuma hukumar ta EFCC.

Leave A Reply

Your email address will not be published.