Wani Soja ya bindige kansa a Abekuta

0
87

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wani soja da ke aiki da Bataliya ta 35 ta Artillery Brigade na sojojin Najeriya a Abekuta, ya harbe kansa har lahira bisa kuskure.

Sojan ya mutu ne sakamakon harbin da ya yi wa kansa bisa kuskure, in ji kakakin runduna ta 81 ta sojojin Najeriya mai kula da bataliyar, Laftanar-Kanar Olabisi Ayeni ya bayyana a ranar Laraba.

Ayeni ya bayyana cewa, da jin ƙarar harbin na bazata, sai abokan aikin marigayin sun garzaya wurin da lamarin ya faru suka same shi a kwance cikin jini kace-kace.

“Tun daga lokacin ne aka fara bincike don gano al’amura da kuma yiwuwar musabbabin faruwar lamarin.

“An ɗauke gawar sojan tare da ajiye ta a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Abekuta,” in ji Mista Ayeni.

Leave a Reply