Sojojin Najeriya sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan’ta’adda, Junaidu Fasagora, da yaransa a Zamfara

0
73

Dakarun rundunar sojin Najeriya da ke yaƙi da ta’addanci a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar sun yi nasarar kashe wani riƙaƙƙen shugaban ƴan’tadda Junaidu Fasagora.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba da daddare, rundunar sojin ta ce ta yi nasarar kashe Fasagora tare da mayaƙansa da dama ne bayan wani zazzafan ba-ta-kashi da aka yi a yankin Tsafe.

“Junaidu Fasagora da ƙungiyarsa ta ta’addanci sun daɗe suna addabar mutane da satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci a al’ummomin jihohi da dama a Arewa maso Yamma,” in ji rundunar.

Ta ƙara da cewa kawar da su ɗin wata muhimmiyar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta’addanci da tayar da ƙayar baya.

Wannan nasara tana zuwa ne sa’o’i kadan bayan da rundunar sojin ta ce ta kawar da wani ɗan’ta’adda ɗaya da ƙwato makamai a wani yanki d aƴan Boko Haram suka yi sansani a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

KU KUMA KARANTA: Na gaya wa Shugaban Ƙasa matsalolin Zamfara kuma ya ba ni tabbacin kawo ɗauki – Dauda Lawal

Sai kuma kisan wasu ƴan ta’addan biyu da ta yi a Garin Rinji da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina bayan musayar wuta da suka yi, inda ta lalata maɓoyar ƴan fashin da kuma ƙwato makamai da wasu kayayyakin.

Jihar Zamfara, inda a can aka kashe Junaidu Fasagora, ta yi ƙaurin suna a wajen tashe-tashen hankula da hare-haren da ƴan bindiga ke yawan kai wa al’ummominta inda suke sace mutane da kashe su.

Ko a farkon makon nan sai da Gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare ya kai wa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke Abuja, inda ya kai masa kukan halin da jihar ke ciki na ta’azzarar rashin tsaro, kuma Shugaban Ƙasar ya ba shi tabbacin kai masa ɗaukin da ya dace.

“Wannan nasarar da rundunar ta samu dai wani ƙarin haske ne na yadda sojojin Najeriya ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da sauran yankunan kasar.

“Sojojin suna ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci, tada ƙayar baya da kuma laifuka daban-daban domin maido da tsaro a yankunan da ake fama da rikici,” a cewar sanarwar rundunar sojin.

Rundunar sojin a baya-bayan nan tana yawan sanar da nasarar da take yi wajen kashe ƙasurguman masu tada ƙayar bayan da suke addabar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar, lamarin da masu sharhi kan tsaro ke yabawa duk da dai suna cewa akwai buƙatar ƙara ƙaimi don kawar da matsalar rashin tsaro baki ɗaya.

Leave a Reply