Kwamandojin Boko Haram biyu sun miƙa wuya bayan shekaru 15 suna tayar da ƙayar baya

0
83

Wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu sun miƙa wuya bayan shafe shekaru 15 suna tayar da ƙayar baya.

Wannan dai wata gagarumar nasara ce da dakarun haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a Gabar Tafkin Chadi ta samu a bayan nan.

Kwamandojin da aka bayyana sunayensu da Ibrahim Muhammed da Auwal Muhammed wanda aka fi sani da Wanka, ‘yan ƙungiyar Bakura Buduma ne da ke kai hare-hare a wurare daban-daban a gabar Tafkin Chadi.

Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: Shugaban mulkin sojan Nijar ya tattauna da Putin kan haɗin gwiwar tsaro

Ya kuma alaƙanta miƙa wuyan da suka yi da yadda dakarun haɗin gwiwar ke gudanar da ayyukansu ba dare ba rana wajen kai wa ’yan ta’addan hare-haren ta sama da kasa babu kakkautawa.

Waɗannan kwamandoji biyu dai su ne masu aiki a tsibiran Tafkin Chadi har zuwa lokacin da suka yanke shawarar ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya.

Laftanar Kanar Abdullahi ya ce yayin da suke amsa tambayoyi, Muhammed da Wanka sun bayyana alakarsu da kungiyar Bakura Buduma na tsawon shekaru 15, inda suke gudanar da ayyukansu a yankin Kwallaram da ke tsibirin Tafkin Chadi.

Rundunar ta MNJTF ta kuma karɓe wasu tarin makamai a hannun mayaƙan da suka haɗa da bindigogi kirar AK-47, alburusai, gurneti, da rediyon hannu, da wayoyin hannu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, mayaƙan da suka miƙa wuya na hannun dakarun sojin domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply