Saboda bikin sallah: Gwamnan Kebbi ya ba da umarnin a biya albashin watan Afrilu

1
1261

Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu ya amince da biyan albashin watan Afrilu ga ma’aikatan gwamnati a jihar nan take.

Amincewar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin shugaban ma’aikatan Safiyanu Garba-Bena kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta ware miliyan 73 don ciyar da masu azumi a watan Ramadan

Ya ce an yi hakan ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho damar gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa cikin sauƙi.

A cewar muƙaddashin shugaban ma’aikatan, tuni bankunan suka fara sakin sanarwar albashi ga ma’aikata kamar yadda gwamnan ya bayar.

1 COMMENT

Leave a Reply