Gwamnatin Yobe ta ware miliyan 73 don ciyar da masu azumi a watan Ramadan

3
222

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da kashe Naira miliyan 73 don ciyar da marasa galihu a ƙarƙashin shirinta na ciyar wa a watan Ramadan na shekarar 2023.

Alhaji Mala Musti kwamishinan harkokin addini na jihar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Damaturu. Ya kuma bayyana cewa samar da dafaffen abinci da gwamnatin jihar ke yi ga mabuƙata a cikin watan Ramadan al’ada ce tun shekarar 1999.

Kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar ta kai buhunan shinkafa 1,050 domin shirin, inda ya ce za a ƙara karbar buhunan shinkafa domin ci gaba da aiwatar da shirin. “Kuɗaɗen da gwamnati ta amince da shi, shi ne Naira miliyan 73, za a yi amfani da su ne wajen sayan raguna da kayan dafa abinci a cibiyoyin ciyar da abinci 67 da aka samar a jihar.

KU KUMA KARANTA: Za mu ci gaba da takatsantsan wajen amfani da dukiyar jama’a – Gwamna Buni

“Mun shirya sanya jami’an mu da za su zagaya domin duba duk wuraren da ake ciyar da abinci; ba za mu iya barin shi haka don mutane su je su yi duk abin da suke so ba, ”in ji Musti.

Ya yi kira ga masu hannu da shuni da su shiga cikin shirin, inda ya ce akwai lada mai yawa wajen ciyar da gajiyayyu musamman a watan Ramadan.

Ya ƙara da cewa, gwamna Buni ya kuma amince da naira miliyan 30 a matsayin alawus ga malaman addinin musulunci domin gudanar da ayyukan ibada daban-daban a cikin lokutan azumi.

3 COMMENTS

Leave a Reply