Real Madrid ta fitar da Man City daga gasar Champions League

0
128

Real Madrid ta yi ramuwar gayya kan Manchester City a filin wasa na Etihad ranar Laraba inda ta fitar da ita daga Gasar Zakarun Turai ta Champions League a wasan kwata-fainal.

Madrid ta doke City, mai riƙe da kofin na UEFA, da ci 4-3 a bugun fenareti bayan sun yi canjaras da ci 1-1 a wasan.

Ɗan wasan Madrid Rodrygo ne ya soma zura ƙwallo jim kaɗan da soma wasan amma daga bisani Kevin De Bruyne ya farke inda kowace ke da ci 1-1 da maki 4-4 jimilla.

Hakan ne ya sa aka tafi bugun fenareti.

KU KUMA KARANTA: Surayya Aminu Za Ta Bunkasa Harkokin Matasa Da Wasanni

Ƴan wasan City sun soma sa ran haɗuwa da Bayern Munich a wasan kusa da ƙarshe lokacin da Luka Modric ya ɓarar da bugun fenaretin Real na farko amma Andriy Lunin ya kaɗe ƙwallayen Bernardo Silva da Mateo Kovacic.

Wannan wasa ya kawo ƙarshen fafatukar da City ke yi ta lashe kofuna uku a kakar wasa ɗaya: Kofun Zakarun Turai, da na Gasar Firimiya da na FA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here