Mutum 19 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Kano

0
333

Wani hadarin mota a Najeriya

Daga Rabo Haladu

Rahotanni daga jihar Kano  sun tabbatar da afkuwar mummunan hadarin mota, a kan hanyar Kano zuwa Zaria, inda mutane 19 suka mutu nan take, 26 suka jikkata.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis a kusa da Makarantar Horas da Aikin Lauya da ke Bagauda a jihar, bayan motoci kirar bas sun yi taho-mu-gama lamarin da ya janyo motocin suka kama da wuta.

Jami’in hulda da jama’a da wayar da kai na hukumar kare hadurra ta Najeriya reshen jihar Kano, SRP Abdullahi Labaran, ya shaida ka  cewa gudun wuce-sa’a da motocin suke yi ne ya haddasa hatsarin.

”Binciken da jami’anmu suka gudanar, sun gano dukkan motocin biyu na haya ne, kuma mummunan gudun da direbobin ke yi ne ya san ya suka kasa sarrafa motocin shi ne suka yi taho-mu-gama.

“Nan take motocin suka kama da wuta, wasu daga cikin fasinjojin ciki har da wadanda suka mutu da jikkata sun kone. Mun mika gawawwakin ga ‘yan uwan mamatan, yayin da sauran aka kai su babban asibitin karamar hukumar Kura da ke jihar domin karbar magani,” in ji jami’in hulda da jama’ar.

Labaran ya kara da cewa suna bakin kokari domin ganin an rage hadurra a Najeriyar, ta hanyar tilasta wa direbobin motocin haya da na gida sanya na’urar da ke takaita gudun mota.

Haka kuma suna kokarin wayar da kan direbobi ta hanyar shiga tashoshin mota, da tuntubar malaman addinai domin fadakarwa.

Ana yawan yin hadarin mota a manyan titunan Najeriya, wanda ake dora alhakin hakan kan rashin kyawun tituna, da tukin ganganci da uwa uba gudun da ya wuce kima da masu ababen hawa ke yi

Leave a Reply