Sarki Sanusi: “Ina Goyon Bayan Rufe Kan Iyakar Najeriya”

0
299

Daga Wakilinmu

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana cewar kasashen da ke mokobtaka da Najeriya ba sa taimaka mata wajen kare tattalin arzikinta.

Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi ya bayyana wa BBC cewar dole ce ta sa Najeriya ta dauki matakin rufe dukkan iyakokinta, domin ta bunkasa tattalin arzikinta musamman abin da ya jibanci noman shinkafa.

Hakan ne ya sa Sarkin yaba wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari kan matakin rufe iyakokin kasar daga shigar da abubuwan da ake iya samarwa a cikinta.

Sarki Sunusi ya kuma sake yaba wa Buhari dangane da kafa kwamitin kwararru domin kula da harkar tattalin arzikin kasar.

A baya dai Sarki Sanusi ya sha sukar gwamnatin Shugaba Buhari bisa gazawa ta fannin tattalin arziki.

Leave a Reply