An Yi Jana’izar Mutane 100 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Zamfara

0
426

Daga Wakilinmu

Rahotanni daga jira Zamfara sun yi nuni da cewa an yi jana’izar akalla mutane 143 sakamakon munanan hare-haren da yan bindiga suka kai a ranakun Laraba da Alhamis kan kananan hukumomin Anka da Bukuyyum na jihar Zamfara. 

A halin yanzu dai ana ci gaba da neman karin gawarwaki mutane sama da 100 kamar yadda wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida mana inda ya ce mutane sama da 200 sun rasa ransa a sakamakon harin.

Rahotannin sun yi nuni da cewa ‘yan ta’addan da ke tserewa sakamakon luguden wutan jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya wanda ya raba su da matsugunin su a dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi, sun yi tattaki zuwa kudancin Zamfara, inda suka afka wa mutanen yankin suka kashe da dama daga ciki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya daga yankin ta shaida cewa ana ci gaba da aikin zakulo wasu gawarwaki daga cikin dazuzzuka.KU DUBA WANNAN MAAmurka Ta Gargadin Yan Kasarta Kan Bulaguro Zuwa Najeriya

Majiyar ta kara da cewa yan bindigar sun afkawa mazaunan kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukuyum bayar wasu a cikin gonaki wası kuma a cikin gidajensu dikin ba’a zata.

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa yan bindigar sun kona gawarwakin wasu daga cikin wadanda al’amarin ya shafa baya fille musu kawunansu inda ba’a iya gane su ma.

A cewar wata majiya, yan bindigar sun kai hare-haren ne ba tare da bari ko tausayawa mata da kananan yara ba inda suka yi ta cinnawa gidajen mutane wuta kuma da zarar mutane citi har da kananan yara da mata suka yi kokain tserewa suna bindige su da kona gawarwakinsu.

A halin yanzu dai mutanen da suka sami nasarar tserewa suna samun mafaka a wasu al’ummomin da suka fi samin tsaro a yanzu.

Rahotanni sun kuma yi nuni da cewa al’ummomin da ‘yan bindigar suka afkawa sun haura 10 kuma miyagun na tafiya daga wannan al’umma zuwa waccan a kan babura suna aikata kisan gilla ga al’ummomin da ba su ji ba su gani ba.

A yayin rubuta wannan labari dai rahotanni sun yi nuni da cewa yan bindigar sun janye amma ba su yi nisa da kauyukan da aka kai farmakin ba.

Leave a Reply