Mutane 20 sun mutu a wani kwale-kwale da ya nutse a gaɓar tekun Senigal

0
45

Masu aikin ceto sun zaƙulo gawarwaki fiye da 20 daga tekun arewacin Senigal a ranar Laraba bayan da wani kwale-kwalen da ke ɗauke da baƙin haure da ke kan hanyar zuwa Turai ya nutse, kamar yadda wani gwamnan yankin ya shaida wa AFP.

Gwamnan yankin Saint-Louis Alioune Badara Samb ya fadi ta wayar tarho cewa, “An gano gawarwaki sama da 20,” ya kuma ƙara da cewa an kuma ceto wasu ƙarin mutane 20.

Badara Samb bai bayyana adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba amma waɗanda suka tsira sun shaidawa AFP cewa adadin ya kai ɗari.

KU KUMA KARANTA:An buƙaci ‘tsawaita wa’adin mulkin’ shugaban Senegal Macky Sall

Mamady Dianfo, wanda ya fito daga Casamance da ke kudancin ƙasar mai nisa, ya ce akwai fasinjoji kusan 300 a lokacin da kwale-kwalen ya tashi daga Senigal mako ɗaya da ya wuce.

Gaɓar tekun Senegal dai wani wuri ne da ake ƙara samun fitowar baƙin haure ‘yan Afirka da ke zuwa tsibirin Canary na Spain, tashar jiragen ruwa na shiga Turai.

Leave a Reply