Ministocin Isra’ila sun yi tir da kuɓutar da marayu da dama daga Gaza da aka yi wa ƙawanya

0
118

Ministocin Isra’ila biyu sun yi Allah wadai da farmakin da sojojin ƙasar suka kai na ceto marayun Falasɗinawa 70 daga Gaza tare da saukaka tura su zuwa Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye bisa buƙatar Jamus.

Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, ofishin jakadancin Jamus da ke Isra’ila ya bukaci Tel Aviv da ta taimaka wajen miƙa yaran marayu daga yankunan da aka yi wa ƙawanya zuwa Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye.

“Wanda ya tausaya wa azzalumi daga ƙarshe zai zama mai zaluntar masu tausayi,” kamar yadda Ministan Kudi Bezalel Smotrich mai tsattsauran ra’ayi ya wallafa a shafin X, yana ambaton wata karin maganar Malaman Yahudu.

KU KUMA KARANTA: ANIsra’ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana

“Ina neman ƙarin haske daga Firaiminista game da wane ne ya ba da wannan umarni na rashin tsari kuma a kan wane iko, yayin da ake garkuwa da mutanenmu da ƴaƴansu a can.”

Ministan Tsaro na ƙasa mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya kira lamarin da “matakin jinƙai na ƙarya.”

Leave a Reply