Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida

1
1759

Kotu ta yi watsi da buƙatar APC da Dakta Yusuf Gawuna na ƙalubalantar zaɓen Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida)

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi watsi da da buƙatar Jami’yyar APC da ɗan takararta na Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na ƙalubalantar nasarar zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

A zaman shari’ar a yau Talata Kotun ta ce APC ba ta bi ƙa’idar shigar da ƙara ba, saboda haka ta yi watsi da buƙatarsu na ƙalubalantar zaɓen.

1 COMMENT

Leave a Reply