Dalilin da ya sa muka kori Ɗanjuma Goje daga APC – Jam’iyar APC

0
556

Daga Ibraheem El-Tafseer

A watan da ya gabata ne jam’iyyar APC a matakin mazaɓa ta kafa wani kwamiti domin binciken zarge-zargen yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa da ake yi wa sanata Ɗanjuma Goje a zaɓukan 2023.

A lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a Kashere, shugaban mazaɓa na jam’iyyar Tanimu Abdullahi, ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin korar sanatan ne bayan da kwamitin binciken ya same shi da laifin da ake zarginsa da shi.

KU KUMA KARANTA: Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida

Ya ce “Daga cikin laifukan zagon-ƙasan da ya yi wa jam’iyyar har da rashin halartar tarukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar,”.

”Da kuma rashin halartar babban taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyar na ƙasa Abdullahi Adamu suka jagoranta”, in ji shi

Leave a Reply