Gwamnatin Kano ta sayo kayan ɗaki ga ma’aurata 1,800

0
271

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan ɗaki da sauran kayan ɗaurin auren ma’aurata 1,800 a ƙarƙashin shirinta na ɗaurin aure.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da ya duba wasu kayayyakin da za a ɗaura auren a ranar Laraba a Kano.

Ya ce gwamnati ta sanya kasafin kuɗi sama da naira miliyan 800 don sayan kayan sawa da kayan abinci da kayan ɗaki da sauran kayan buƙatu na bikin aure.

“Kowace Amarya za ta karɓi katifa da matashin kai, da kuma naira 20,000 domin fara sana’a.

“Wasu masu hannu da shuni sun yi alƙawarin bayar da gudummawar kason su don ganin an samu nasarar ɗaurin auren.

“Ma’aurata 1,800 za su amfana da wannan karimcin, wanda zai taimaka matuƙa wajen daƙile munanan ɗabi’u da fatara a tsakanin al’umma, saboda an ɗage auren da yawa, saboda gazawar iyaye wajen ɗaukar nauyin ɗaurin auren,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Kano ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da auren jinsi

Malam Daurawa ya ce za a sanar da ranar ɗaurin auren ne domin baiwa mazauna yankin da kuma ɗaiɗaikun mutanen da ke son taimakawa su ba da gudummawar kason su don cimma burin da ake so.

Ya ƙara da cewa, an gindaya sharuɗɗa na zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, ya ƙara da cewa waɗanda suka saki matansu bisa rashin uzuri bayan auren, za su biya gwamnati kuɗin su.

Leave a Reply