Gwamna Fintiri ya jagoranci shiga tsakani kan batun Shaikh Idris Dutsen Tanshi

0
195

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Umaru Fintiri, ya jagoranci shugabannin ƙungiyar Izala wajen kai wa takwaransa na Bauchi Gwamna Bala Mohammad ziyara game da taƙaddamar Shaikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.

Gwamna Fintiri ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa shi da Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe da kuma Shaikh Abdulwahab Kano sun kai ziyarar a ƙoƙarin “kawo ƙarshen shari’ar da ake yi wa Shaikh Dutsen Tanshi”.

“Ina matuƙar godiya ga Gwamna Bala Mohammed bisa fahimtarsa ​​da hikimarsa wajen ji daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, da manufar samar da zaman lafiya,” in ji Fintiri.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ba da belin Dakta Idris Dutsen Tanshi bisa sharaɗi

A nasa ɓangaren, Gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewa addini abu ne mai sammatsi da ya kamata mutane su kula.

Ya kuma yaba wa malaman bisa fahimtarsa da kuma Dakta Idris Abdul’aziz da suka yi.

A baya-bayan nan ne aka sako fitaccen malamin, Shaikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi daga gidan yari, bayan ya shafe tsawon kwanaki a wata ƙara da ta shafi zargin aikata saɓo da ake yi masa, na kalaman ɓatanci da rashin ɗa’a da ya yi akan fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Leave a Reply