Dala Biliyan 10 zan ware don inganta rayuwar matasa tare- Atiku Abubakar

1
218

Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa idan ya yi nasara a zaɓen 2023, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 don bunƙasa rayuwar matasa tare da samar da ayyuka, ƙanana da matsakaitan masana’antu da kuma sana’o’i.

A cewar Atiku Abubakar waɗannan zunzurutun kuɗin za su kuma yi amfani wajen tallafa wa mata da matasa kaiwa ga matakan nasarar da su ke ta hanƙoron ganin sun cimma.

A yayin da ake kamfen a jihar Kwara

Atiku ya sha wannan alwashi ne a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, lokacin da ya je yaƙin neman zaɓe a jihar.

Mataimakin shugaban ƙasa a shekarun 1999 zuwa 2007, ya ɗora laifin matsalar tsaro a kan gwamnatin APC.

Ya ce gwamnatin Buhari ta gaza kuma ta yaudari ‘yan Najeriya a fannin tsaro da ayyukan gina ƙasa.

Da ya ke J nuna damuwar sa kan matsalolin jihar Kwara, Atiku Abubakar ya nuna takaici ya ce duk da jihar Kwara ce mahaɗar Arewa da Kudu, amma ba ta da hanyoyi masu kyau.

Yadda matasa suka hallarci taron

Shi kuwa Shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu, cewa ya yi “jam’iyyar PDP babban gida ne wanda kawunan dukkan iyalan gidan a haɗe su ke.kuma tana kan hanyar kaiwa ga nasara.

KU KUMA KARANTA: Zaɓen 2023: An tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC

“PDP za ta dawo ta ceci Nijeriya, ta maida ta kan turbar bunƙasa da ceto”

“Kada ku bari wasu su yaudare ku, yunwar da ta yi mana katutu a yanzu ta nunka wadda mu ka sha a 2015.

“Kowa ya fito da katin zaɓensa, ku zaɓi PDP, ku zaɓi ɗan takarar ta Atiku Abubakar a zaɓen 2023,” inji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply