Burkina Faso ta kori jami’an diflomasiyyar Faransa uku bisa zargin ‘zagon ƙasa’

0
45

Ƙasar Burkina Faso ta kori wasu jami’an diflomasiyyar Faransa guda uku saboda zarginsu da aikata “ayyukan zangon ƙasa”, a cewar wata takardar sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta aika zuwa ofishin jakadancin Faransa.

An ayyana jami’an uku a matsayin “waɗanda ba a maraba da zamansu” kana an ba su sa’o’i 48 da su bar Burkina Faso, in ji sanarwar.

Tun bayan hamɓarar da gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar a watan Satumban 2022, gwamnatin mulkin soji ta nesanta kanta daga Faransa wadda ta yi wa ƙasar mulkin mallaka har zuwa shekarar1960.

Gwamnatin ta soke yarjejeniyar soji da aka ƙulla na shekarar 1961 tsakanin kasashen biyu, sannan ta kori jakadan Faransa a ƙasar bayan juyin mulkin.

A ranar 1 ga watan Disamba, aka kama wasu jami’an Faransa huɗu, kana aka gurfanar da su a gaban kotu, tare da ɗaure su a gidan yarin Ouagadougou da ke babban birnin ƙasar, a cewar wata majiya ta Faransa.

KU KUMA KARANTA: An kashe aƙalla mutum 170 a Burkina Faso

Hukumomin Burkina Faso sun ce jami’an leƙen asiri ne amma majiyar Faransa ta ce ma’aikatan da ke taimaka wa fannin ililmin fasaha na IT ne.

Yanzu haka dai mutanen huɗu suna tsare a gida a cewar majiyoyin tsaron Burkina Faso.

A watan Disambar 2022, Ouagadougou ta kori wasu Faransawa biyu da ke aiki a wani kamfanin Burkina Faso bisa zarginsu da leƙen asiri.

Kasar Faransa ta kawo ƙarshen ayyukan soji da ke yaƙi da masu jihadi a Mali da Burkina Faso

Sannan a baya-bayan nan ta soma janye dakarunta daga Nijar – ƙasashe ukun da a halin yanzu ke ƙarƙashin gwamnatin mulkin soji bayan juyin mulkin da suka yi.

Burkina Faso dai ta ƙara karkata zuwa ƙasar Rasha da Mali da Nijar domin neman taimakon tsaro.

Leave a Reply