Ba mu da shirin haɗe wa da jam’iyar APC – ‘Yan Kwankwasiyya

0
101

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta ce kawo yanzu babu wanda ya tuntuɓeta game da shiga jam’iyyar APC.

Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, ya shaidawa BBC cewa wannan ƙira ake cewa shugaban APC Ganduje ya yi musu a kwararo suka ji shi.

”Mun ji bayanin cewa ya miƙo wannan ƙoƙon bara na gwamna ya dawo jam’iyyar APC to amma abin mamaki shi ne, shi Ganduje a matsayinsa na tsohon gwamna da tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake isarwa gwamna mai ci saƙo idan ana son ya je wurinsa”, in ji Sanusi.

Ya kuma ƙara cewa gwamna Abba Yusuf ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko ƙin barin jam’iyyarsa.

”Amma maganar da muka ji ya faɗa, a kafafen yaɗa labarai na zumunta mu ka ji ta, kuma a nan mu ka barta’’

”Ka san ita siyasa ko in ce sauya sheƙa ta siyasa kamar canza gida ne, ba ka tashi lokaci ɗaya kawai ka ɗauki jakarka ka fita, ka ce wai ka canza gida.

KU KUMA KARANTA: Dalilanmu na shiga zawarcin ‘yan kwankwasiyya da jagoransu – Ganduje

“Akwai abubuwan da za ka iya yi kafin ka ce ka canja gida saboda don haka mu a wurinmu wannan saƙo mun ji ne kawai kamar a sama”, in ji shi.

Wannan yunƙuri na jam’iyyar APC na zuwa ne bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, na cewa ɓangarorin biyu su je su sasanta da juna.

Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.

Leave a Reply