Ba a ga watan sallah a Najeriya ba

0
46

Kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce ba a samu ganin jinjirin watan Shawwal ba a yau Litinin, 29 ga watan Ramadan.

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce Sarki Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya amince da rahoton kwamitin.

KU KUMA KARANTA: Ba a ga watan ƙaramar Sallah ba a Saudiyya

Saboda haka ya yi matsaya cewa watan Ramadan zai cika kwanaki 30 kuma ranar Laraba 10 ga watan Afrilu, ita za ta kasance 1 ga watan shawwal kuma ranar sallah karama a Najeriya

Ba wannan ne karon farko da ake yin Azumi talatin ba a Najeriya.

Leave a Reply