An kai ƙarar Zomo ofishin ‘yan bijilante a Kano

0
536

Wani matashin manomi Musa Garba da ke garin Ɗorawar Sallau, a ƙaramar hukumar Kura, jihar Kano, ya kai ƙarar Zomo ofishin ‘yan Bijilanten yankin, har ma kuma ya sa yara su ka taimaka masa wajen yin tara-tara, suka kama Zomon, ya damƙashi a hannun ‘yan Bijilante.

A ta bakin mai Zomon, Musa Garba ya ce, dama Zomon fitinanne ne, ya dade yana dauko masa magana, hasali ma tun da ya bar gida kwana da kwanaki yana neman sa.

Mai magana da yawun ƙungiyar bijilante din yankin, Uba Muhammad ya ce, sun sulhunta manomin da mai Zomon, bisa sharadin za a kai shi kasuwar Kura a sayar da shi.

Har yanzu dai hukumomin da ke kula da kare hakkin dabbobi ba su komai ba, dangane da al’amarin.

Leave a Reply