An kama ‘yan bigilante da laifin kashe wani mutum a Jihar Kano

0
280

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano ta tabbatar da cafke wasu jami’an bijilanti 6 bisa zarginsu da lakaɗawa wani mutum duka wanda hakan yai sanadiyar mutuwar sa. Tun a ranar 31 ga watan da ya gabata na 2022 lamarin ya faru a yankin Unguwar Kankare dake Rijiyar Zaki ,wanda aka ga mutumin mai suna Musa Lawan ɗauke da wani jariri a hannunsa wanda mutane suka rufe shi da duka.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan samun rahotanne muƙaddashin kwamishinan yan sandan jahar Kano DCP Abubakar Zubairu ya tura tawagar yan sanda waɗanda suka garzaya da mutumin da kuma jaririn zuwa babban Asibitin Murtala dake Kano wanda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka jami’an bijilanti 6 suna hannunsu a sashin binciken manyan laifukan kisan kai dake Bompai kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za su sanar da halin da ake ciki.

Leave a Reply