AN DAKATAR DA  YQJIN AIKIN DIREBOBIN BABURA MASU KAFA UKU A KANO

0
302

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

BAYANAN da muke samu daga Jihar Kano na cewa yayan kungiyar Direbobin da ke sana’ar tukin Babura masu kafa uku da ake kira Keke Nafef sun Dakatar da yajin aikin da suka fara tun ranar Litinin da ta gabata.

Rahotannin da muke samu daga Jihar Kano na cewa dakatarwar ta biyo bayan zaman tattaunawa ne da aka yi tsakanin Lauyoyin yayan kungiyar direbobin Keke Nafef da kuma Manajan Daraktan hukumar kula da kiyaye dokokin ababen hawa wato KAROTA, Baffa Babba Dan Agindi, a ranar Larabar nan.

Taron tattaunawar tsakanin bangarorin biyu dai ya dauki tsawon watanni uku ana yinsa, karkashin jagorancin Aminu Sani Gadanya, shugaban kungiyar Lauyoyi (NBA) ta Jihar Kano.

Za mu kawo maku ci gaban duk wani bayanin da ya samu nan gaba.

Leave a Reply