An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi

4
483

Hukumar kula da ‘yan wasan tsalle-tsalle ta sanar da dakatar da ‘yar wasan tsere ta Najeriya, Grace Nwokocha, saboda zargin amfani da ƙwayoyin da aka haramta.

Athletics Integrity Unit (AIU) ta dakatar da ‘yar wasan mai shekara 21 wadda ke cikin tawagar ‘yan mata huɗu da suka lashe lambar zinare a gasar ƙasashen rainon Ingila ta 2022 a wasan tsere na tsallake shinge.

Hukumar ta ce an samu ɓurɓushin ƙwayoyin Ostarine da Ligandrol a cikin jinin Nwokocha bayan gwajin da aka yi mata.

“AIU ta dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nzubechi Grace Nwokocha saboda amfani ko kuma samun ƙwayoyin da aka hana amfani da su a jikinta (Ostarine da Ligandrol),” a cewar hukumar cikin wata sanarwa a shafinta na Twitter.

Hakan na nufin ba za ta sake shiga wasanni ba har sai an yanke hukuncin ƙarshe yayin zaman da za a yi ƙarƙashin jagoranci da dokokin hukumar hana zamba a wasanni ta WADA.

Ana fargabar akwai yiwuwar a ƙwace kyautar zinariyar da Najeriya ta samu a tseren.

4 COMMENTS

Leave a Reply