An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen maye gurbin Sanatan Yobe ta Gabas

0
109

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen maye gurbin Sanatan Yobe ta gabas da za a yi.

Ganduje ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin a lokacin ƙaddamar da gagarumin gangamin yaƙin neman zaɓen Sanatan Yobe ta Gabas a filin wasa na ‘August 27’ da ke birnin Damaturu.

Da yake jawabi ga dandazon mahalarta taron, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya ba da tabbacin ayyukan jam’iyyar na ƙasa wajen bayar da dukkanin goyon bayan da suka dace domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a mazaɓar Yobe ta gabas.

Ya kuma bayyana cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gamsu da sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar kwanan nan.

Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce kasancewar shugabannin jam’iyyar na nuna muhimmancin taron yaƙin neman zaɓen APC.

Buni ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da ci gaban jihar.

Shi ma da yake jawabi, shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya yi ƙira ga masu zaɓe a jihar da su kaɗa ƙuri’a cikin hikima domin samun sahihin zaɓe domin samun ci gaba, kwanciyar hankali da ci gaban jam’iyyar a jihar.

Ya bayyana cewa, Musa Mustapha shi ne ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen 2024 mai zuwa na Sanatan Yobe ta gabas.

Gadaka ya kuma karɓi wasu jiga-jigan waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP, APGA da NNPP zuwa jam’iyar APC.

KU KUMA KARANTA: A karon farko a tarihi, mace ta zama shugabar ƙaramar hukuma bayan lashe zaɓe a jihar Borno

Babban taron jam’iyyar APC mai wakiltar Yobe ta Gabas ya samu halartar tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Ibrahim Lawan, ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Ozodima da Khadija Bukar Abba Ibrahim da sauran ‘yan siyasa a faɗin jihar ta Yobe.

Leave a Reply