Allah Ya Jikan Hajiya Umma Zaria

0
316

Daga; Jabiru Hassan Dungurawa.

A MATSAYINA na mutumin jihar Kano, Ina mai amfani da wannan kafar labarai domin in jaddada addu’a ta ga kakarmu Hajiya Umma Zaria, mahaifiya ga Alhaji Aminu Alhassan Dantata bisa rasuwar ta.

Babu shakka, wannan baiwar Allah ta aikata abubuwa na alheri Kuma masu ban mamaki duk da cewa ba kowa yasan hakan ba. Sannan tayi bakin kokarin ta wajen sada zumunci da hada kan dangi bisa la’akari da muhimmancin zumunci da kaunar juna.

Allah ya gafartawa Hajiya Umma Zaria da maigidan ta Alhaji Alhassan Dantata ya jaddada rahama a garesu da daukacin musulmi da suka riga mu gidan gaskiya. Haka Kuma Ina Mai amfani da wannan dama domin taya maigirma Alhaji Aminu Alhassan Dantata murnar cikar sa shekaru 91 a duniya tare da fatan ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

Jabiru Hassan Dungurawa, Karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.
(jabiru.hassan@yahoo.com)

Leave a Reply