Muhimmmancin Makarantun Kimiya Da Fasaha Da Yadda Za Su Cicciba Najeriya Sama

0
372

Daga; Auwal Ahmed Ibrahim (Goronyo)

KAMAR yadda kusan kowane dan Najeriya ya sani ne cewa ilmin makaratun firamari a Najeriya musamman na Gwamnati ta zama tamkar mushan gizagi a wasu garuruwa inda mafi yawan dalibai a makarantu ba su da gurin zama, babu ofisoshin malamai ga kuma rashin makewayoyi masu kyau da tsafta duk da irin makudan kudade da gwamnatoci suke warewa a kowane mataki, to amma wannan bai hana ilmin makarantun kananan makarantun gwannati tabarbarewa ba.

A wata hira da aka yi da shugaban hukumar Ilmin Kimiya da Fasaha ta kasa, Farfesa Idris M. Bugaje a gidan rediyon Rhythm FM, Abuja, ya bayyana cewa inda ba don gwagwarmaya da jan tunga da kungiyoyin malaman makarantun manyan gaba da sakandire suke yi ba da ilmin jami’o’in Najeriya ya zama ba banbanci da ilmin makaratun firamari badan.

Sai dai kuma masana na ganin kudaden da gwannati ke warewa bai wuce cikin cokaliba na abun da ya kamata ta kasheba wajan farfado da ilimi musamman a matakin farko a kasar nan.

Bukatar Hukumar kyautata Ilimi da kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) shi ne ga kowace kasa ta ware kaso kashi 26 na kasafin kudin ta ga ilimi. Amma a Najeriya a shekara ta 2021 kaso biyar zuwa shida aka ba bangaran ilimi, hakazalika a shekarata 2022 da ake ganin ya kamata a ma ilimi rikon dan amaryar, Inda sashen Ilimin ya sami kashi 14 cikin dari dan farfado da ilimin bayan irin jibgar da annobar Cuta mai Shake Numfashi (Corona Virus) ta yi ma ilimin a kafatanin fadin duniya.

Ilimi baya tafiya yadda ya kamata har sai malamai sun sami kulawa amma mafi akasarin malaman Najeriya cikin tsaka mai wuya suke inda su kan kasance a tsakiyar kura da siyaki.

Wasu malamai ko a jami’o’i ba su da ofisoshin da za su zauna su gudanar da ayyukan su, haka tashin gwauron zabi da rayuwa ta yi ta jefa malamai da yawa cikin ni’yasun kuncin rayuwa duk da irin kokarin su na tabbatar da sun bayar da ilimi kamar yadda ya kamata wajan sauke nauyin da aka daura masu.

Kamar dai yadda aka sani ne cewa ilmi shi ne gishirin rayuwar da yake saka rayuwa dadi, badan malamai ba, da rayuwa ta kara muni da kunci. Ilmi shi yake taimakon kowane dan-adam ya gina rayuwarsa har ya haskama wasu fitila domin shi kansa ilimi kan samar da aiki ga dunbin al’ummar kasa, sai dai wani kuskure da yake karama kwabar Najeriya ruwa a bangaran ilimi shi ne wuce makadi da rawa da ake yi wajan yawaitar jami’o’i a Najeriya fiye da makarantun kimiya da fasahohi wadanda manufar su shi ne koyar da sana’o’in hannu a zahiri.

Farfesa Idris M. Bugaje yana da tunani da yakini na cewa idan makaratun kimiya da fasaha suka fi yawa kuma aka inganta su a kasar nan, za a sami raguwar fitintunun da su ka ma kasar daurin laimon minti, haka kuma ayyuka za su wadatu a kasar har jama’ar kasar su fantsama cikin duniya domin fafutukar neman halaliyar su a wasu kasashe cikin kima da kulawa.

A Najeriya, kiyasi ya nuna cewar akwai makarantun kimiya da fasaha guda 69 a inda ake da kimanin jami’o’i guda 170 wanda abun da ake gani wannan shi ne barin reshe a Kama ganye.

A cewar Farfesa Bugaje, kwalejojin kimiya da fasaha suna da kaifi biyune wajan Cicciba kasa ga tudun muntsira baya ga horar da dalibai ilmi, kuma akwai horo da sukan iya ba ‘yan kasuwa masu aikin hannu dan samun Takardun shaidu da za su iya aiki da su a ko’ina a fadin duniya koda kuwa ma ba su taba shiga aji ba. Haka kuma a ka’ida daliban makarantun kimiya da fasaha ya kamata su fi yawa dan kuwa a duk karkashin wani shugaba a gurin aiki da ake bukata a ma’aikata ko gurin aiki ana bukatar masu tallafawa guda biyar wadanda suka sami horo daga kwalejojin kimiya da fasaha.

Ko shakka babu, ilimin kimiya da fasaha shi ne zai iya tsayar da Najeriya a kan bigiran kasashen duniya wadanda suka tsaya da dugadugin su amma samuwar haka kan iya tabbatuwane kadai idan gwannati ta bayar da fifiko da kulawa ga makarantun kimiya da fasaha a kasar nan dan tabbatar da Najeriya kasar da zata dinga cin gashin kanta ba a matsayar saniyar tatsa ba.

Hukumar Kula da Makarantun Kimiya da Fasaha ta Najeriya, NBTE ita ce madogara a daidai wannan lokaci da Najeriya take kokarin samun mafuta ga matsalolin da suka mata katutu da makoko.

Kamar yadda masanan ilmi da addini suka tabbatar cewa tsaro baya samuwa a tsakanin al’ummar da yunwa take ci kamar wutar daji. A daidai irin wannan lokacin da Najeriya take kukan targade da karaya, gwannati ba zata iya share ma jama’a hawaye ba har sai kowa ya mike dan yakar talaucin da yake bude da baki kamar zaki. Koyan sana’a yana da kyau amma zuwa makarantar da zata ba da shaidar koyan aiki shi ne mafi a’ala.

Fasalin manhajar karatun makarantun kimiya da fasaha shi ne yake bayar da sa’ar baro tsuntsu biyu da dutse daya, tun mutun yana dalibi yakan iya fara cin moriyar karatun sa kafin kammalawa, in kuwa ya kammala ya samu takardar yakan iya samun aiki.

Damar da NBTE take da shi na horar da masu sana’o’in hannu da bayar da shaida, abu ne da zai tsayar da kasar nan a kan turbar mun tsira ga masu sha’awar kara daukaka kan su a sana’o’in su domin kuwa a dukkanin kowace sana’a, buncike shi yake kara daukaka a kanta.

Iyaye da dalibai, ya kamata su fahimci, makarantun kimiya da fasaha ya kamata su runguma domin cigar da kasar nan gaba da kuma samun dogaro da kai domin dai bukatar maje haji sallah.

Sai dai kuma dan rungumar wannan kudiri sai fa gwannati ta gane muhimmanci da alherin da ke ciki tumbul tartare da makarantun kimiya da fasaha wajan gina kasa da gina al’umma. Haka samar da kayan koyan karatun da horarwa za su taimaka gaya wajan fardodo da kimar makarantun kimiya da fasaha a Najeriya, sannan da so samu ne daliban makarantun kimiya da fasaha in basu zama wadanda za su dunga amsar albashi mafi tsoka ba, to su zama daidai da dukkanin daliban jami’o’i a kowane fanni kila ko shakka wannan ne zai kara kima da martabar makarantun kimiya da fasaha a Najeriya.

Auwal Ahmed Ibrahim (Goronyo)
Malami ne a Kwalejin Kimiya Da Fasaha Ta Kaduna A Sashen Koyar Da Aikin Jarida

Leave a Reply