Kafofin Yada Labarai Ne Ke Kan Gaba Wajen Bayar Da Gudunmuwar Zaman Lafiya – Fatima Agwai

0
269

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

AN bayyana kafofin yada labarai a matsayin wata muhimmiyar hanyar da ke kan gaba wajen bada Gudummawa domin tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma, domin sai an samu zaman lafiya ne tattalin arziki da harkokin rayuwar jama’a za su inganta.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin babbar jami’ar kula da labarai na Hukumar kula da hakkokin bil-Adama NHRC, Hajiya Fatima Agwai Mohammed a yayin kaddamar da kasidar ta a wajen taron Horar da ‘yan jarida kan harkokin wayar da kan jama’a wanda ya gudana gudanar a garin Yola fadar gwamnatin Jihar Adamawa.

Taron horaswaan an gudanar da shi ne dangane da yanayin gudanar da yafiya da daidaito musamman ga ‘yan Gudin Hijirar Boko Haram da kuma ‘ yan ta’addan da suka tuba dake son shigowa cikin al’umma, musamman a Jihohin Yobe, Borno da Adamawa.

Fatima Agwai ta kara da cewa Hukumar su ta NHRC ba za ta taba cimma nasarar ayyukan ta ba face sai da taimakon ‘yan jaridu domin sune ke bayyanawa jama’ a dukkan abubuwan da ke gudanuwa.

Don haka tana kara kalubalantar manema labarai da su ci gaba da nunawa al’umma muhimmancin yafiya a tsakanin juna wanda ta yin hakan za a samu yanayin zaman lafiya mai inganci a tsakanin al’umma.

Har ila ta kuma bayyana cewa, akwai bukatar da kafofin yada labarai da su ci gaba da bada sahihan labarai da zai taimaka wajen kara inganta yanayin zaman lafiya ba labarin da zai kara rura wutar rikici ba.

A karshe, Hajiya Fatima Agwai, ta yaba wa kafofin yada labarai da manema labarai dangane yadda suke ba su goyon bayan domin samu nasarar ayyukan su kasancewar ba za su iya taba cimma nasarar ayyukan su ba, ba tare da goyon bayan su ba.

Leave a Reply