Hukumar NHRC Ta Fara Horar Da ‘Yan Jaridu Kan Muhimmancin Yin Sulhu Da Adalci Ga Al’umma

0
315

Daga; Sani Gazas Chinade, Yola.

HUKUMAR Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa (NHRC) ta fara horar da ‘yan jaridu a yankin Arewa maso Gabas kan inganta sulhu, sake hadewa da tabbatar da adalci a tsakanin al’umma.

Kamar yadda Wakilin mu ya ruwaito cewa, horon wanda wani shiri ne na gwaji da Tarayyar Turai ta dauki nauyin gudanar da shi, ana gudanar da shi ne a Yobe, Borno, da kuma Adamawa tare da hadin gwiwar hukumar ci gaban Majalisar Dinkin Duniya UNDP.

A jawabin da ya gabatar a taron horaswar da ake yi a fadar gwamnatin Jihar Adamawa dake Yola a ranar Litinin, Babban Sakataren Hukumar NHRC, Tony Ojukwu, ya ce aikin na gwaji shi ne bullo da tsarin da al’umma za su jagoranta don tabbatar da adalci da sulhu ba tare da shari’a ba a matsayin ginshikin sake hadewa da kuma dawo da zaman lafiya Arewa Gabas.

Ojukwu wanda ya samu wakilcin Mista Hilary Ogbonna, jami’in kula da ayyukan, ya bayyana cewa, gudanar da adalci zai taimaka wajen hanzarta hanyoyin waraka da baiwa wadanda abin ya shafa da kuma al’umma damar yin adalci da sulhu tare da dawo da tsaffin mayakan Boko Haram da su mika wuya cikin al’ummomin su.

Babban Jami’in, ya lura cewa nasarar shirye-shiryen bayan rikice-rikicen zai dogara ne a kan dabarun bayar da shawarwari da sadarwa wadda kafofin yada labarai na da rawar takawa matuka.

Ya kara da cewa hakan zai sa al’umma su rungumi sulhu a matsayin ginshikin farfadowa da ci gaban zaman lafiya a wannan yanki na Arewa maso Gabas.

“Kafofin yada labarai na taka muhimmiyar rawa wajen yada labarai, wayar da kan jama’a da kuma tsara ra’ayoyin jama’a.”

“Saboda wannan muhimmiyar rawa da kafofin yada labarai ke takawa musamman wajen inganta adalci dangane da gudanar da zaben sulhu a yankin Arewa maso gabas ya sa a kullum muke yaba musu.”

“A cewar sa babu wani kokari da bai kamata a yi watsi da shi ba wajen bunkasa karfin kwararrun kafafen yada labarai don rungumar wannan aiki da kuma gudanar da wannan aiki yadda ya kamata,” in ji Ojukwu.

Ya kara da cewar, ana sa ran horar da ‘yan jarida a Jihohin da rikicin ya shafa, da dai sauransu, zai kara karfafa kwarin gwiwar kwararrun kafafen yada labarai a kan manufar tabbatar da adalci da kuma wajibcinsa na ganin bayan rigingimu a yankin Arewa maso Gabas.

Da ya ke jawabi Babban Lauyan Jihar Adamawa, Mista Samuel Yaumande da Sakatare-Janar na Ma’aikatar Sake Gine-gine, Gyara da bada Agajin gaggawa na Jihar Adamawa, Misis Aishatu Umar, sun bayyana aikin a matsayin wanda ya dace da lokacin da ‘yan gudun hijirar suka koma yankunan iyaye da kakanni.

Sun jaddada kudirin gwamnatin Adamawa na tallafawa ainihin ‘yan Gudin Hijira da kuma’ yan Boko Haram din da suka tuba suka kuma mika wuya da komawa ga al’ummar su.

Takardun da aka gabatar a ranar farko ta horon sun hada da “Gudunmawar kafofin yada Labaru wajen samar da zaman Lafiya, Sulhu da Adalci.

Sauran sun hada da Gudunmawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen inganta hanyoyin sasantawa da sake hadewa da juna a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya bayan tashe-tashen hankula da Karfafa amincewar al’umma da juriya wajen karbar tsoffin ‘yan Boko Haram da suka koma gida.

Shi ma a nasa jawabin dangane da muhimmancin kafofin yada labarai dangane da rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya a wannan yanki na Arewa maso Gabas.Dakta Jude A. Momodu, Darakta a cibiyar kula da yanayin zaman lafiya da harkokin tsaro da ke jami’ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama da ke Yola, ya jaddada Muhimmancin kafofin yada labarai ga al’umma a duk wani rikici da kan iya faruwa a tsakanin al’umma.

A cewarsa, in aka lura da rikici ko kuma yakin da ya afku a wasu yankunan duniya da suka hada da Rwanda, Sabiya da kuma uwa uba yakin duniya na biyu yadda ya Adolf Hitler ya yi amfani da kafofin yada labaransa wajen yada farfagandar yaki da sauran su.

Don haka akwai bukatar kafofin yada labarai da su ci gaba da ayyukan su na wayar da kan jama’a muhimmancin da ke akwai dangane da yafiya da kuma samar da Adalci a tsakanin juna.

Ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi tun fara rikicin Boko Haram kimanin kusan shekaru 13 da suka gabata don shawo kan al’ummar da suke ganin ana cutar da su dangane da wannan rikici don su yafe wa juna musamman ga wadanda suke ganin an cutar da su an kashe musu mutanen su a ce kuma wadanda suka aikata musu wannan irin ta’asa za a dawo da su cikin su don ci gaba da rayuwa kamar kowa yin hakan na bukatar kafofin yada labarai taka muhimmiyar rawa kamar yadda suka saba wajen wayar da kan jama’a don amincewa da su, yin hakan zai sa a samu kyautatuwar zaman lafiya mai daurewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here