Connect with us

Labari

Hukuncin Kotu Ya Tabbatar Da Zan Iya Tsayawa Takarar Gwamna – Isa Ashiru

Published

on

Daga; Imrana Abdullahi, Kaduna.

GABANIN lokacin zaben fitar da Gwani a Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, dan takarar Gwamnan Jihar, Honarabul Isa Mohammd Ashiru ya bayyanawa manema labarai cewa hukuncin da babbar kotu ta yanke ta wanke shi zai iya tsayawa takarar fitar ga Gwanin.

Tsohon dan majalisar wakilan, Isa Ashiru ya ce hukuncin da wata babbar kotu ta yanke kwanan nan inda ta Kori karar baki daya a matsayin mara tushe da aka gina a kan jita-jita jita kawai, cewa Isa Ashiru ba shi da takardun makaranta balantana ya samu damar cika sharadin tsayawa takarar Gwamna, wanda wani dan jam’iyyar PDP mai suna Isa Abdullahi, ya kai karar karya ne.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis, daraktan kula da harkokin shari’a na kwamitin neman zaben Honarabul Isa Ashiru, Barista Husaini Abdu cewa ya yi bayan an wanke shi kuma ya cancanci tsayawa takara.

Ya ce “muna tattara sunayen wadanda suka yi wa dan takarar mu batanci da nufin daukar matakin doka sai dai in har sun yi abin da ya kamata na wallafa bayanin ban hakuri a cikin manyan jaridun kasar nan masu fita a kullum da daukar matakin cewa sun yi Nadama da irin abin da suka aikata, zamu iya zafe musu”.

Shi wanda ya shigar da kara a gaban wata babbar kotu a Zariya Isa Abdullahi, cewa ya yi Honarabul Isa Ashiru bashi da takardun makaranta da zai tsaya takarar Gwamna a Jihar Kaduna don haka ya gabatarwa da kotu kararsa.

“Amma Ashiru ya gabatar da korafin kalubalantar wannan kara inda ya ce hakika ya cancanci tsayawa takara domin ya na da ingantattun takardu saboda haka nema ya bukaci a biya shi batanci har kudi naira miliyan daya (1) domin bata masa suna.

Honarabul Isa Ashiru ya gabatar da takardun makaranta guda shida da suka hada da satifiket na kammala karatun sakandare da aka bashi a shekarar 1980 da ya kammala kwalejin Kufena, Zariya. Sai takardar karatun Difiloma ta kasa da kuma babbar Difiloma da ya kammala daga kwalejin limits da fasaha, sai kuma shaidar kammala karatun PGD da shaidar kammala karatun digiri na uku a bangaren karatun gudanar da mulki daga jami’ar Bayero da ke Kano.

Kamar dai yadda Lauya Abdu, ya ce a ranar 9 ga watan Mayu 2022, alkalin babbar kotu M. K. Dabo ya kori karar baki daya.

An Kori karar ba ma wai an yi watsi da ita ba, don haka ba za a iya dawo da ita kotu ba kenan har abada sai dai idan an daukaka kara, kuma a iya sanin mu har yau ba a daukaka karar ba.

“Wanda ya yi karar ya cika wani bangare na hukuncin da aka yi da kotu ta bukaci a wallafa bayanin bayar da hakuri a jarida amma har yanzu bai wallafa na biyu ba kuma bai biya kudin da kotu ta bukata ya biya wanda yake kara ba”.

Dan takarar Gwamna Isa Mohammad Ashiru zai yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da an samu nasarar zaben fitar da dan takara.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labari

EMAS69 • LINK ALTERNATIF SPORTBOOK SBOBET

Published

on

By

Emas69 adalah bandar taruhan sportbook sbobet terlengkap yang saat ini sangat dikenal seluruh masyarakat Indonesia dengan melalui link alternatif Emas69. Pada permainan taruhan sportbook, setiap pertandingan sepak bola yang dilangsungkan dapat dijadikan sebagai tempat bagi seluruh masyarakat Indonesia untuk melakukan taruhan dengan menggunakan uang asli. permainan taruhan bola online dapat dilakukan dengan bebas sesuai dengan pertandingan yang berlangsung dan juga team sepak bola yang disenangi untuk memperoleh kemenangan dan kepuasan dari setiap taruhan sportbook di situs Emas69.

Continue Reading

Labari

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Published

on

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like