Ansace Mutane Da Dama A Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

0
338

Daga; Rabo Haladu.

MASU garkuwa da mutane sun sace mutane da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.

Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci.

Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a kan ɓangaren zuwa Kaduna da ɓangaren dawowa da aka yi awon gaba da masu motocin.

Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗumbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami’an tsaro sun yi musayar wuta da yan bindigar amma babu ƙididdiga ta mutanen da aka sace.

Leave a Reply