Hukumar Jami’an Tsaron NSCDC Kaduna Ta Samu Sabon Shugaba

0
300

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

HUKUMAR Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence (NSCDC) ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, ta samu sabon Shugaba a Jihar, kwamanda Idris Yahya Adah.

Sabon Shugaban Yahya Adah, ya Karbi akalar ragamar Jagorancin hukumar ne bayan da tsohon kwamandan Dakta Godwin U Miebi ya yi ritaya daga aiki a ranar 10 ga Mayu 2022.

A yayin kayatccen bikin mika mulkin ga Kwamanda Idris Yahya Adah wanda ya Karbi ragamar jagorancin kwamandan a ranar 11 ga Mayu 2022, an yi musayar tuta bayan an kammala binciken Qartergaurd.

A yayin da jawabi ga Jami’an, Adah ya godewa babban kwamandan Janar Dakta Abubakar A. Audi mni bisa amincewar da suka yi masa tare da yin alkawarin yin bakin kokarinsa na ganin an ciyar da hukumar gaba a Jihar.

Ya kuma bukaci Jami’an da su gudanar da ayyukansu cikin himma tare da gujewa duk wani aiki na tashin hankali da rashin da’a.

Kwamandan Idris ya kuma roki mutanen Jihar Kaduna da su taimaka wa rundunar wajen samar da bayanai masu amfani da kuma bada goyon baya wajen taimakawa hukumar (NSCDC) wajen samar da isasshen tsaro a jihar.

Kwamandan ya nemi hadin kan ‘yan jarida tare da karfafa masu gwiwa da su rika tantancewa da buga bayanai kawai wadanda za su samar da hadin kai a tsakanin al’umma da kasa baki daya.

Ya yi alƙawarin cewa haɗin gwiwa da aka riga aka kafa tsakanin hukumar NSCDC da sauran Hukumomin da ake jin daɗinsu a cikin jihar, za a ƙara ci gaba da inganta su ne kawai.

A karshe, Kwamandan Idris ya kammala da cewa NSCDC za ta yi aikinta ba tare da nuna wata tsangwama ba, kana tare da goyon bayan gwamnatin Jihar da duk masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply