Ɗalibai a faɗin Amurka na ci gaba da yin zanga-zangar nuna adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza

0
56

Yayin da ɗalibai a faɗin Amurka ke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza, wasu sun yi Allah wadai da shugabannin Jami’ar Columbia da ke New York saboda ƙira wa masu zanga zangar jami’an tsaro a makon da ya wuce.

Ɗaliban da ke zanga-zangar nuna adawa da yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas a jami’o’i a faɗin Amurka, inda wasunsu suka yi arangama da ‘yansanda, sun kafa sun tsare a yau Asabar kuma sun sha alwashin ci gaba da yin zanga-zangarsu, yayin da sassan jami’o’i da yawa suka yi Allah wadai da shugabannin jami’o’in da suka nemi jami’an tsaro su fatattaki masu zanga-zangar.

Yayin da Jami’ar Columbia ke ci gaba da yin shawarwari tare da ɗaliban da ke zanga zangar goyon bayan Falasɗinawa a harabar makarantar da ke New York, majalisar zartarwar Jami’ar ta sanya hannu a wani ƙudirin a ranar Juma’a wanda ya kafa wani kwamiti da zai yi bincike akan shugabancin jami’ar, wacce a makon da ya gabata ta ƙira ‘yansanda don su wargaza masu zanga-zangar, lamarin da ya haifar da arangama ya kuma kai ga kamen mutane fiye da 100.

KU KUMA KARANTA:Amurka za ta janye dakarunta daga Chadi

Duk da cewa Jami’ar ta sha sanya wa’adin ta da dandalin masu zanga zangar ta kuma ɗage shi, Jami’ar ta aika da wani saƙon Email ga ɗalibai a daren ranar Juma’a mai cewa sake kawo ‘yansanda makarantar “a wannan lokacin” ba zai yi tasiri ba, saƙon ya ƙara da cewa suna fatan tattaunawar da ake yi zata kawo ci gaba.

Yayin da adadin waɗanda suka mutu a yaƙin Gaza ke ƙaruwa, masu zanga-zanga a faɗin Amurka na neman makarantu su yanke hulɗar kuɗi da Isra’ila su kuma ƙaurace wa kamfanonin da suka ce suna assasa rikicin.

Wasu ɗalibai Yahudawa sun ce zanga zangar ta na rikiɗewa ta koma nuna ƙyamar Yahudawa kuma suna fargaban shiga harabar makarantunsu.

Leave a Reply