Zamu Samar Da Taki Sama Da Tan Dubu 130 Ga Manoma A Daminar Bana- Musa Sallau

1
383

Daga; Rabo Haladu.

KAMFANIN sarrafa taki na Namalale, ya yi alkawarin samar da Takin zamani tan dubu 130 ga manoma a daminar bana ga manoma dake Arewacin kasar nan baki daya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Manajan Kamfanin, Umar Sallau Musa, jim kadan bayan kungiyar ‘yan jarida na Arewa Ta NUJ ta karrama kamfanin da lambar yabo bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen samar da Taki mai inganci da samawa matasa aikin yi a fadin Arewacin kasar baki daya.

Manajan ya ce sun shirya tsaf domin samar da wadataccen taki ga manoma cewa wanda zai zama mai inganci daidai da yanayin kasar noman da ake da ita, bisa farashi mai sauki.

Ya ci gaba da cewa a wannan daminar bana, kamfanin zai samar da taki sama da Tan dubu 30 kwatankwancin buhu dubu dari da talatin 130 domin amfanar manoma a daminar bana.

Umar Sallau, ya bayyana cewa kamfaninsu ya kudiri aniyar samar da takin zamani mai inganci da Nagarta wanda duk manomin da yayi amfani dashi zai samu yabanya mai yawa.

Acewarsa kamfaninsu na samar da aikin yi ga matasa masu yawan gaske wadanda suke aiki kai tsaye da kamfanin zuwa ‘yan sarin kayansu da kuma ‘yan talla, wanda mafiyawan wadanda zasu amfana manoma ne, da matasa masu neman sana’a.

Da yake mika lambar yabon ga manajan kamfanin, Shugaban Kungiyar ‘yan jaridar Alhaji Mukhtar Maitama, ya ce sun karrama kamfanin Namalale ne bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ciyar da kasa gaba ta bangaren bunkasa harkokin noma.

Shugaban wanda Sani Haladu ya wakilta ya ce Kungiyar ‘yan jaridu na Arewacin Najeriya sun gamsu da yadda Kamfanin takin Namalale yake gudanar da ayyukansa na bunkasa harkokin noma a fadin kasar nan baki daya.

Daga karshe kungiyar ta bukaci kamfanin da ya dauki lambar yabon a matsayin wani kalubale wajen ci gaba da abubuwan da suka saba.

1 COMMENT

Leave a Reply