‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane 40 Bisa Tozarta ‘Yan uwansu Masu Keke-napep

3
453

Daga Rabo Haladu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano  ta ce ta kama kimanin mutum 40 bisa zargin afka wa wasu masu sana’ar babur mai kafa uku, saboda kin shiga yajin aikin da suke yi, tare da yi wa masu tafiya a kafa kwace.

Tun dai da safiyar Litinin aka girke jami’an tsaro na ‘yan sanda da na rundunar tsaro ta civil Defense wasu daga cikin manyan titunan Kano, don jiran ko ta kwana na yiwuwar samun rikici a lokacin da masu babur mai kafa uku a jihar suka fara yajin aiki.

A cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, mutanen da suka kama suna dauke da makamai inda suke tare hanya suna yi wa mutane kwace da tilasta wa masu kananan motoci daukar kaya sauke mutanen da suka dauko don rage musu hanya.

3 COMMENTS

  1. Ya Allah yakyauta da wannan irin hastaniya da ta kefaruwa a kano gawannan yaji aiki da kuma raderadinda ake akan many an ya’n siyasar kwan kwaso da Ganduje

Leave a Reply