‘Yan sanda a Ondo, sun ƙuɓutar da ‘yan cocin CAC takwas da aka yi garkuwa da su

0
199

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ce ta ceto wasu Kiristoci guda takwas da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su da yammacin ranar Juma’a a Elegbeka da ke ƙaramar hukumar Ose a jihar.

Mutanen da aka sace ‘yan Cocin Christ Apostolic Church, CAC, Oke Igan, Akure, babban birnin jihar ne.

An ce waɗanda lamarin ya rutsa da su na tafiya ne a cikin motar cocin zuwa Ifon da ke yankin ƙaramar hukumar Ose a jihar domin yin jana’izar, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai su daji.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an ƙuɓutar da waɗanda harin ya rutsa da su ba tare da jin rauni ba.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun ƙubutar da mutane 25 daga Boko Haram

Mista Odunlami-Omisanya ya ce waɗanda aka ceto mata bakwai ne da namiji ɗaya, yayin da ake ƙoƙarin ceto wasu ba tare da samun rauni ba.

“Albishir!, An ceto mutane 8 da harin ya rutsa da su, ana ci gaba da ƙoƙarin ceto wasu da ba su ji rauni ba.

“Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun ce suna kan hanyarsu ta zuwa wurin kwana; A lokacin da suka isa Ajagbale ta Elegbeka akan titin Ifon/Owo, wasu ‘yan bindiga biyar ne suka kama su inda suka yi harbe-harbe da ƙarfi suka tafi da su cikin daji,” inji ta.

Leave a Reply