Yadda yajin aikin ASUU ya chanja min tunanina, daga Abubakar M Taheer

0
323

Tun bayan Tsunduma yajin aiki da malaman jami’o’i sukayi kimanin watannin Uku da suka shude,
Na fara tunanin Wata hanya ce zan bi domin ribatar wannan lokaci na zaman gida.

Ni Dalibine dake ajin Karshen A Jami’a (500L) wannan tasa nayi dogon nazarin sanarwar kaina mafita da kuma tunkarar rayuwa gaba gaɗi.

Mahaifina ya daukin zunzurutun kudin makaranta ya bani domin biyan kudin karatu.

Na duba ga kudi ga yajin aiki, dayake ina Sana’ar dogaro da kaina ta Chajin Waya A garinmu.

Haka tasa Na haɗa da kudin makaranta da ɗan wanda nake samu a kasuwa na Karbi hayar gona domin noman shinkafa yar rani.

Kamar wasa na tanaji komai da ake bukata nama biya kudin hayar gona Naira dubu ashirin na dukufa nake zuwa gona kamar da Take ka fatata ta chanja zuwa baka saboda wahala.

‘Yan watanni kafinnan, munyi magana da Aunty na Dake Abuja, wanda Take Digirin digirgir ta bani shawarar daukan hanya mai ɓullewa domin samun cigaba rayuwa wannan tasa nake jin kamar anamin allurar soja wajen zuwa gona.

A haka nake shiga cikin mutanen kauye muke Caƙuduwa dasu muna idan naje Ban ruwa inayi ina ciran ciyawa.

Haka suke gwada min Rike Sprayer domin fisarar maganin kwari, Kamar Perfect Killer da Sauransu.

Idan ban sanar da kai cewa nasan Kalamar turanci daya ba, bazaka taba iya ganewa ba saboda irin kokarin danake wajen yin aiki.

A yanzu Noman shinkafa musamman ‘yar rani yana da kashe kudi kama daga Man fetur wanda duk bayan kwana biyu ko uku nakan siyi na dubu biyu zuwa sama.

Ga kuma uwa uba taki wanda nasiya daga ragowar kudin s makaranta da maigidanmu ya bani duk kudin ya tafi a yin Harrow,jiko,dashe dss.

Shagon chaji kar Dan uwansa Dalibin jami’a ya dauka a rufe yake, a’a akwai yaron da yake tattara mana taro da kwabo wanda duk wanda ya sani ya san karamar sana’a ce samun ta baikai ya kawo ba.

Abinda aka ɗan samu shine za’a siyi mai da kuma biyan kudin masu ciran ciyawa dadai sauransu. A haka aka kwashe watanni ana turawa, shinkafa ‘Yar rani Wata uku takeyi kwana casa’in, daga nan Saide kaji ana Zancen dubu daruruwan.

Misali Idan ka samu buhu Ashirin, yanzu haka ana saida kowanne dubu goma sha takwas kaga (18,000*20)=N360,000

Idan kuma ka samu sama da haka kaga kudin ya tafi.

Yanzu haka ‘yan kwanaki ya rage A bugeta a kwashe Riga a kuma cire uwar kudin.

Duk kuma a wannan lokacin daga fara yajin aikin ASUU zuwa Yau.

Shawara gareka abokina dalibin jami’a Yanzu damana ta sauka Ruwan sama ya samu kayiwa kanka karatun tanutsu, Ka nemi gona koda ta tudu ce(Gero,dawa, masara) ka noma kaine da riba.

Idan kuma yankinku da ruwa ana noman shinkafa ka Nemi gonar shinkafa ka noma .

Ana samun Miliyoyin kudi a noman Shinkafa dana Tudu a wannan zamani.

Kaine da riba, idan ASUU sun dawo Masha Allah idan basu dawo ba kaga kasami abinda Bature yake cewa Plan-B na gina rayuwarka.

Lokacin da ASUU zasu dawo Saide kaji kana Lissafin Miliyoyin a hannunka kaga Kana gama karatu Ka samu Hanyar dogaro dakai har wani ma yaci a ƙasanka.

Kaida kake da burin Gina rayuwarka kada ka bata lokacinka, Ka sani lokaci tamkar takwabine na yaki idan baka yi amfani dashi wajen yaƙi ba shi zai yake ka.

Ka sani Cewa” Time waits for no one,Time Stops for no one, your Excuses will not slow down time,Your Indecisions will not delay Time,Your Complaining will not stall time,Your regrets will not turn back Time”.

Na Barka lafiya Dan uwana dalibin Jami’a.

Aluta Kwantiniyo!!! Victoria Asata!!!.

Leave a Reply